Rahotanni sun ce a kalla mutane 56, yawancinsu ‘yan kasuwa, sun mutu yayin da wasu 14 suka jikkata a wani harin jirgin sama da ya auku a kasuwar Jilli da ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin ya faru ne a ranar Asabar a kasuwar da ke tsakanin Gubio a jihar Borno da kuma Geidam a jihar Yobe, wadda ke tara ‘yan kasuwa daga yankuna daban-daban na jihohin biyu.
Majiyoyi sun ce harin na iya kasancewa ɓangare na farmakin soja kan waɗanda ake zargi ‘yan Boko Haram ne, amma jirgin ya kauce daga inda aka tsara ya kai harin ya fada kan fararen hula.
Wani ganau ya ce an tabbatar da mutuwar mutane 56, yayin da 14 ke kwance ana jinyarsu a Asibitin Kwararru na Geidam. Haka kuma, jami’an yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar ta Daily Trust.
Jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki sun ce ana ci gaba da bincike kan lamarin domin tantance hakikanin abin da ya faru da kuma adadin wadanda abin ya shafa.