Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kwastam ta kama fetur da fatar jaki da kudinsu yakai naira miliyan 98.3 a Adamawa da Taraba

Custom Kwastam ta kama fetur da fatar jaki da kudinsu yakai naira miliyan 98.3 a Adamawa da Taraba Custom Kwastam ta kama fetur da fatar jaki da kudinsu yakai naira miliyan 98.3 a Adamawa da Taraba

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama man fetur da aka yi safararsa ba bisa ƙa’ida ba tare da fatar jakuna da darajarsu ta kai naira miliyan 98.375 a jihohin Adamawa da Taraba cikin makonni shida.

Mataimakin kwanturola Janar, Aminu Tako, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce nasarar ta samu ne sakamakon bayanan siri da yaki da safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce an kama kayayyakin a wurare daban-daban, inda a ranar 26 ga Fabrairu, 2026 aka cafke buhuna 43 na tsofaffin kaya da wasu kayayyakin haram a kan hanyar Savannah–Numan.

Haka kuma a ranar 12 ga Maris, 2026, jami’an sun kama fatar jakuna 509 da kuma naman jaki busasshe kilo 460 a kan hanyar Mubi–Sangere.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use