Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, na shirin gabatar da muhimmin jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki kan tsarin zaɓen Najeriya.
Za a gudanar da taron ne a ranar 29 ga Afrilu, 2026 a birnin Abuja, ƙarƙashin jagorancin kamfanin lauyoyi na Law Corridor.
Taron zai haɗa shugabannin jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula, da kuma masu sa ido kan zaɓe na cikin gida da na ƙasashen waje domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi inganta tsarin zaɓe a ƙasar.
Manufar taron ita ce nazari kan manyan ƙalubalen da ke fuskantar tsarin zaɓen Najeriya, tare da gano hanyoyin da za a bi wajen magance su yadda ya kamata.
Masu shirya taron sun bayyana cewa an tsara wannan zama ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban gabanin babban zaɓen shekarar 2027.