Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Khalil: Kwankwaso ba jagoran ADC ba ne a Kano

Khalil: Kwankwaso ba jagoran ADC ba ne a Kano Khalil: Kwankwaso ba jagoran ADC ba ne a Kano
Khalil: Kwankwaso ba jagoran ADC ba ne a Kano

Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar ADC zeben 2023, Sheikh Ibrahim Khalil, ya jaddada kudurinsa na sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

A wata hira da ya yi da Explorer Hausa, Khalil ya bayyana cewa daukar wannan mataki babban nauyi ne da al’ummar Kano suka dora masa, kuma yana ganin wajibi ne ya amsa wannan kira.

Ya kuma karyata rade-radin da ke cewa jam’iyyar ADC na fama da rikici a jihar Kano, inda ya ce babu wata babbar matsala face sabanin ra’ayi tsakanin bangaren Nafiu Bala Gombe da na David Mark, wanda a cewarsa abu ne na dabi’a a siyasa.

Dangane da zargin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya mamaye jam’iyyar a Kano, Khalil ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

Ya bayyana cewa Kwankwaso memba ne kamar kowa, kuma yana daya daga cikin jagororin jam’iyyar a jihar, amma ba shi ne jagoran ta ba.

Khalil ya kara da cewa duk wani kaso da aka bai wa Kwankwaso a cikin jam’iyyar, za a raba shi ne tare da Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya shigo jam’iyyar a baya-bayan nan.

Haka kuma, dan takarar ya yi suka ga gwamnatin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya ce akwai kura-kurai da dama da yake da niyyar gyarawa idan ya samu dama.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use