Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Jinya a ƙasashen waje na haddasa asarar makudan kuɗaɗe a Najeriya

Jinya a ƙasashen waje na haddasa asarar makudan kuɗaɗe a Najeriya Jinya a ƙasashen waje na haddasa asarar makudan kuɗaɗe a Najeriya
Jinya a ƙasashen waje na haddasa asarar makudan kuɗaɗe a Najeriya

Wasu ‘yan Najeriya sun soki gwamnati kan yawaitar tafiya ƙasashen waje domin neman magani, suna mai cewa hakan na jawo asarar makudan kuɗaɗe tare da nuna raunin tsarin kiwon lafiya na cikin gida.

Rahotanni sun nuna cewa ƙasar na rasa biliyoyin daloli a kowace shekara sakamakon “zuwa kasashen waje jinya”, inda masu hali da wasu jami’an gwamnati ke fifita jinya a waje maimakon asibitocin gida.

Masana sun ce wannan na raunana tattalin arziki, tare da ƙara matsin lamba ga darajar naira, sakamakon fitar kuɗaɗe zuwa ƙasashen waje.
An danganta matsalar da ƙarancin kayan aiki, rashin ƙwararru, da kuma rashin amincewar jama’a da asibitocin cikin gida.

Sai dai masana sun jaddada cewa ƙarin zuba jari da inganta harkar lafiya zai taimaka rage asarar da ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na ƙasa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use