Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

CITAD ta gargadi NBC kan barazanar ‘yancin ‘yan jarida

CITAD ta gargadi NBC kan barazanar ‘yancin ‘yan jarida CITAD ta gargadi NBC kan barazanar ‘yancin ‘yan jarida
CITAD ta gargadi NBC kan barazanar ‘yancin ‘yan jarida

Cibiyar fasahar bayanai da ci gaba (CITAD) ta soki sabon umarni da hukumar kula da kafafen watsa labarai (NBC) ta bai wa gidajen rediyo da talabijin, tana mai cewa hakan na barazana ga ‘yancin faɗar albarkacin baki a Najeriya.

Kungiyar ta ce umarnin na iya takaita aikin ‘yan jarida, musamman saboda wasu ƙa’idoji marasa cikakken bayani da za su iya hana su sukar gwamnati ko masu iko.

CITAD ta kuma yi gargadin cewa hakan na iya haifar da tsoro a cikin aikin jarida, inda masu gabatar da shirye-shirye za su guji tattauna muhimman batutuwa saboda tsoron hukunci.

A ƙarshe, ta buƙaci NBC da gwamnati da su janye umarnin tare da buɗe tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin kare ‘yancin ‘yan jarida da inganta dimokuraɗiyya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use