Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata rahotanni da ke zargin ana ɓoye ko karkatar da kuɗaɗen gwamnatin tarayya, tana mai cewa an yi kuskuren fassara sakamakon rahoton ci gaban tattalin arzikin Najeriya na Bankin Duniya.
Cikin wata sanarwa da ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya fitar, gwamnati ta ce yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke fassara rahoton ya mayar da tsarin kasafin kuɗi na doka tamkar ɓarna ko satar kuɗi.
Ta bayyana cewa cire-ciren kuɗaɗen FAAC ba wani laifi ba ne, domin sun haɗa da halastattun kashe kuɗi kamar tallafi ga jihohi, kuɗaɗen tsaro, da kuma biyan kuɗi ga hukumomin gwamnati.
Gwamnatin ta kuma zargi wasu masu sharhi da amfani da tsofaffin bayanai, tare da yin watsi da sabbin gyare-gyaren da ake aiwatarwa domin ƙara gaskiya da inganta harkar kuɗaɗen shiga.
Ta ce akasin yadda wasu ke fassara shi, rahoton Bankin Duniya ya nuna alamun ingantuwa a tattalin arzikin Najeriya, inda hauhawar farashi ke raguwa, tattalin arziki ke bunƙasa a fannoni daban-daban.