Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwar wayar talho a ƙasar da su fara biyan diyya ga kwastomominsu ta hanyar ƙarin katin kira (airtime), a duk lokacin da aka samu rashin ingancin sabis.
Wannan umarni na zuwa ne bayan hukumar ta tabbatar da cewa wasu yankuna a faɗin ƙasar na fama da matsalolin katsewar kira, raunin siginar sadarwa, da jinkirin intanet, lamarin da ke janyo matsala ga harkokin kasuwanci da mu’amalar yau da kullum na jama’a.
A cewar NCC, manufar wannan sabon tsarin ita ce tabbatar da cewa masu amfani da sabis ba sa ɗaukar nauyin gazawar kamfanonin sadarwa kaɗai, musamman idan aka kasa samar da ingantaccen sabis kamar yadda ka’idojin aiki suka tanada.
Hukumar ta bayyana cewa za a rika ƙididdige diyya bisa tsawon lokacin da aka samu matsalar da kuma irin tasirin da ta yi ga masu amfani, inda za a tura ƙarin kati kai tsaye zuwa layukan da abin ya shafa.
Haka kuma, NCC ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido sosai kan ayyukan kamfanonin sadarwa a ƙasar, tare da ɗaukar matakan ladabtarwa ga duk wanda ya karya ƙa’idojin ingancin sabis.
A ƙarshe, hukumar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na inganta harkokin sadarwa a Nijeriya da kuma kare haƙƙin masu amfani da sabis a duk faɗin ƙasar.