’Yan bindiga sun kai hare-hare a Bamako babban birnin Mali da kuma wasu wurare da dama a fadin ƙasar kamar yadda sojoji suka bayyana.
Kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban ne suka hada kai wajen kai wannan farmakin na karshen mako.
Sojojin sun ce suna fafatawa da kungiyoyin da suka kira “yan ta’adda” da safiyar Asabar bayan sun kai hari kan barikin sojoji a Bamako da sauran yankuna.
Rahotanni sun nuna cewa an ji karar harbe-harbe tun kafin karfe shida na safe kusa da sansanin soji na Kati, wanda ke wajen Bamako, kuma nan ne mazaunin shugaban mulkin sojin kasar Janar Assimi Goita.
Wani dan jarida ya ruwaito cewa an yi amfani da manyan makamai da kuma bindigogi masu sarrafa kansu a kusa da filin jirgin sama na Modibo Keita da ke Bamako.
Masana sun bayyana cewa irin wannan shiryayyen hari mai girma bai saba faruwa ba a Mali.
Kasar ta shafe sama da shekaru goma tana fama da rikice-rikicen tsaro, ciki har da hare-haren kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda da ISIS, da kuma ‘yan tawaye na kabilar Tuareg a arewacin kasar.