Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
‘yan bindiga sun kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar Mali
‘Yan bindiga sun kashe Ministan Tsaron Mali Sadio Camara – Al Jazeera

‘Yan bindiga sun kashe Ministan Tsaron Mali Sadio Camara – Al Jazeera

Mutuwar camara ta zo ne a daidai lokacin da Mali ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki. (Hoto: AFP) Mutuwar camara ta zo ne a daidai lokacin da Mali ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki. (Hoto: AFP)
Mutuwar camara ta zo ne a daidai lokacin da Mali ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki. (Hoto: AFP)

An kashe Ministan Tsaron ƙasar Mali, Janar Sadio Camara, yayin wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai kan sansanonin soji a sassa daban-daban na ƙasar, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa Al Jazeera.

Rahoton da ya fito a ranar Lahadi ya zo ne kwana guda bayan an kai hari gidansa da ke sansanin soji na garin Kati.

Camara ya kasance jigo a gwamnatin sojin da ta karɓi iko da Mali bayan juyin mulki biyu da suka faru a shekarun 2020 da 2021.

Sojojin Mali sun shafe shekaru sama da biyar suna yaki da ‘yan bindiga a sassa daban-daban na kasar (Hoto: AFP)

Masana tsaro da siyasa na cewa mutuwarsa babbar illa ce ga rundunar sojin ƙasar wacce ke yaki da ‘yan bindiga.

Maharan sun kai hari ne ta amfani da motar kunar bakin wake a gidan Camara da ke Kati, wani gari mai tsauraran matakan tsaro na soji da ke kimanin kilomita 15 a Arewa maso yammacin babban birnin ƙasar, Bamako.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use