Rahotanni daga Gaza sun bayyana cewa wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wani asibiti a birnin Gaza ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
An ce harin ya faru ne a kusa da asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, inda wani Bafalasɗine ya rasa ransa, yayin da aƙalla mutane uku suka jikkata—lamarin da wasu ke ganin ya saba yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kafafen yaɗa labarai na Falasɗinu sun ruwaito cewa harin ya fara ne da luguden wuta kan wani gida da ke kusa da asibitin a yammacin ranar Juma’a, kafin daga bisani sojojin Isra’ila su ƙara harbe-harbe a yankin.
A wani hari na daban, an jikkata wasu mutane bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari da ababen hawa a yankin al-Mawasi, da ke yammacin Khan Younis a kudancin Gaza.