Wani jigon jam’iyyar ADC kuma tsohon ɗan Majalisar Dattawa daga jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya ce zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu idan aka gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci.
Melaye ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Mic On Podcast wanda Seun Okinbaloye ke gabatarwa, inda ya jaddada cewa babban burinsa a yanzu shi ne tallafa wa duk wani ɗan takara da zai fito daga haɗakar siyasa.
Ya ce, “Ɗan’uwana, duk wanda ke cikin masu neman shugabancin ƙasa a ADC zai fi Tinubu sau miliyan ɗaya aiki. Ba za su taɓa zama mafi munin shugabanni fiye da Tinubu ba.”
Ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa Shugaba Tinubu zai iya shan kaye idan aka gudanar da zaɓe mai cike da gaskiya da adalci, yana mai cewa shi kansa zai iya kayar da shi idan ya tsaya takara.
Ya ce, “Ni, Dino Melaye, mu je zaɓe na gaskiya da adalci,” yana mai ƙarawa da cewa zai iya kayar da shi “da gagarumin rinjaye a Najeriya.”
Sai dai ya bayyana cewa a yanzu ba burinsa na kashin kai ne ya fi muhimmanci ba, illa haɗin kai wajen kawar da gwamnatin da ke kan mulki ta hanyar haɗaka ko yarjejeniya.