Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnati ta yi wa ‘yan Najeriya alkawarin sabunta fata, amma abin da suka samu shi ne sabuwar wahala

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa rahoton IMF ya tabbatar da wahalar da ‘yan Najeriya ke ciki.

Ya ce halin da ake ciki a Najeriya “wahala ce da aka tsara aka yi mata ado da sunan gyara,” saboda munanan manufofi da raunin shugabanci.

Cikin sanarwar da mai tallafa masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce rahoton IMF bai zo da wani sabon abu ba, illa ya tabbatar da abin da ‘yan Najeriya ke rayuwa da shi.

Ya ce an yi wa ‘yan Najeriya alkawarin sabunta fata, amma abin da suka samu shi ne sabuwar wahala—mai tsanani, mai dorewa, yana mai cewa gwamnati na ƙin amincewa da matsalar da ƙasa ke ciki.

Atiku ya ce albashin yazu ba shi da daraja, kasuwanni sun cika da kaya amma ba a iya saye, rayuwa kuma tana cike da wahala da tsanani.

Ya bayyana cewa duk da hauhawar farashin mai a duniya, talauci na ƙara tsananta a Najeriya saboda hauhawar farashin abinci, tsadar sufuri da kuma faduwar darajar Naira.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use