Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sheikh Gadon Kaya: Sulhu na rage rigingimun aure a kotu

Sheikh Gadon Kaya: Sulhu na rage rigingimun aure a kotu Sheikh Gadon Kaya: Sulhu na rage rigingimun aure a kotu
Sheikh Gadon Kaya: Sulhu na rage rigingimun aure a kotu

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abdallah Usman (Gadon Kaya), ya bayyana cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalolin aure da dama ba tare da an kai su kotu ba.

A wata hira da ya yi da Explorer Hausa, malamin ya ce sulhu da shawarwari na addini na taimakawa wajen rage yawan shari’o’i da ke cika kotuna a Najeriya.

Ya ce a mafi yawan lokuta, sabanin da ke tsakanin ma’aurata ana warwaresu cikin sauki ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Sheikh Abdallah ya kuma bayyana cewa mata sun fi maza yawan kawo korafe-korafen matsalolin aure, yana mai cewa hakan na faruwa ne saboda yadda ake sauraron su da kulawa domin nemo mafita.

Ya kara da cewa wannan tsarin sulhu na ci gaba da taimakawa wajen daidaita zaman aure da kuma rage matsin lamba a kotunan Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use