Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

ADC ta karyata zancen fara tattaunawa da jam’iyyar PRP

ADC ta karyata zancen fara tattaunawa da jam'iyyar PRP ADC ta karyata zancen fara tattaunawa da jam'iyyar PRP
ADC ta karyata zancen fara tattaunawa da jam'iyyar PRP

Jam’iyyar ADC ta karyata rahotannin da ke cewa tana tattaunawa da jam’iyyar PRP dangane da hukuncin kotu da ake jira.

Ta ce babu wata irin tattaunawa da kowace jam’iyya a halin yanzu, tare da jaddada cewa tana mayar da hankali ne kan kalubalantar matakin da ta kira haramtacce da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da wasu bangarori suka dauka a kanta.

ADC ta bayyana cewa burinta shi ne kare doka da oda da kuma tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a Najeriya.

Jam’iyyar ta kuma ce tana maraba da hadin kan ‘yan adawa, amma ba za ta janye daga nauyin da ke kanta ba a wannan lokaci.

Don haka, ta bukaci jama’a su yi watsi da jita-jitar cewa tana shirin barin ADC, tana mai cewa tana da yakinin bangaren shari’a zai yi adalci.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use