Jam’iyyar ADC ta karyata rahotannin da ke cewa tana tattaunawa da jam’iyyar PRP dangane da hukuncin kotu da ake jira.
Ta ce babu wata irin tattaunawa da kowace jam’iyya a halin yanzu, tare da jaddada cewa tana mayar da hankali ne kan kalubalantar matakin da ta kira haramtacce da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da wasu bangarori suka dauka a kanta.
ADC ta bayyana cewa burinta shi ne kare doka da oda da kuma tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a Najeriya.
Jam’iyyar ta kuma ce tana maraba da hadin kan ‘yan adawa, amma ba za ta janye daga nauyin da ke kanta ba a wannan lokaci.
Don haka, ta bukaci jama’a su yi watsi da jita-jitar cewa tana shirin barin ADC, tana mai cewa tana da yakinin bangaren shari’a zai yi adalci.