Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojoji sun tarwatsa bam da aka dasa a hanyar Gajiram a Borno

Sojoji sun tarwatsa bom da aka dasa a hanyar Gajiram a Borno Sojoji sun tarwatsa bom da aka dasa a hanyar Gajiram a Borno
Sojoji sun tarwatsa bom da aka dasa a hanyar Gajiram a Borno

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun gano tare da tarwatsa wani bam na hannu da aka dasa a kusa da ƙofar fita ta garin Gajiram, a kan hanyar Maiduguri a Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:09 na dare a ranar 21 ga Afrilu, lokacin da ƙungiyar kwararru masu lalata bama-bamai ta gano na’urar yayin sintiri na yau da kullum.

Inda nan take aka killace bam ɗin tare da tarwatsa shi cikin tsari mai kyau domin kauce wa wata illa ga fararen hula da sojoji da ke yankin.

Bayan haka, dakarun sun ci gaba da bincike da sintiri a yankin domin tabbatar da cewa babu wata barazana da ta rage.

Hukumomin soja sun ce matakin na nuna ƙwarewa da shirin da sojoji ke da shi wajen dakile barazanar ‘yan ta’adda, duk da cewa har yanzu tsaron yankin na buƙatar kulawa sosai.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use