Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnati ta fara shari’ar wadanda ake zargi da shirin kifar da mulki a Najeriya

Gwamnati ta fara shari’ar wadanda ake zargin da shirin kifar da mulki a Najeriya Gwamnati ta fara shari’ar wadanda ake zargin da shirin kifar da mulki a Najeriya
Gwamnati ta fara shari’ar wadanda ake zargin da shirin kifar da mulki a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta shigar da tuhume-tuhumen cin amanar ƙasa guda 13 a gaban kotun tarayya da ke Abuja kan wasu da ake zargi da shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Daga cikin waɗanda ake zargin akwai wani tsohon Manjo Janar na rundunar soja, tsohon Kyaftin a rundunar ruwa, jami’in ‘yan sanda mai mukamin Inspekta, tare da wasu mutane uku da ake zargi da hannu a cikin shirin.

Rahotanni sun nuna cewa hukumomin tsaro sun kammala bincike kan wannan zargi, inda aka ce an shirya kifar da gwamnati ta hanyar amfani da ƙarfi, abin da ya haddasa kama mutane da dama.

Binciken ya bayyana cewa kimanin mutane 40 ake zargi da hannu a wannan makarkashiya, ciki har da jami’an tsaro da fararen hula da ake zargi da taka rawar gani a shirin.

An kama jami’an soja 16 bisa zargin hannu kai tsaye, yayin da aka kama fararen hula biyu kan zargin aikin leƙen asiri, wasu biyu kuma ana zargin an ɗauke su domin tada hankalin jama’a su ƙi bin doka, yayin da wasu biyar ake zargi da taimakawa wajen samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su.

Ana sa ran shari’ar za ta ci gaba a gaban kotu yayin da gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da hukunci kan waɗanda ake zargi da hannu a wannan shiri.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use