Ana ci gaba da matsa lamba ga shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, da ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon zarge-zargen da ke yawo na nuna goyon baya ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyoyin fararen hula da masu sa ido kan zaɓe sun bayyana cewa ci gaba da wannan cece-ku-ce na iya rage amincewar jama’a ga sahihancin hukumar zabe, musamman gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A ranar Litinin, ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje tare da matasan jam’iyyar ADC sun gudanar da zanga-zanga a ofishin INEC da ke Legas da kuma a gaban majalisar dokokin ƙasar Burtaniya, suna neman shugaban hukumar ya sauka.
Haka kuma, wata ƙungiyar farar hula mai suna Movement for Credible Elections (MCE), ƙarƙashin jagorancin manyan mutane irin su Farfesa Pat Utomi, Usman Bugaje, Femi Falana (SAN) da Oby Ezekwesili, ta yi kira ga Amupitan da ya yi murabus domin kare martabar dimokuraɗiyya.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da INEC ta musanta zargin da ke alaƙanta shugaban nata da wani asusun sada zumunta na X (Twitter), tana mai cewa zargin ba shi da tushe.