Shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Buba Marwa, ya bayyana cewa yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na zama babbar barazana ga tsaro, tattalin arziki da kuma zamantakewar Najeriya.
Marwa ya yi wannan bayani ne a wani taro da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada cewa matsalar shaye-shaye ba ta tsaya kan masu amfani da ita kawai ba, har ma tana shafar al’umma da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na lalata tunanin matasa tare da hana su samun ci gaba a rayuwa, yana mai gargadin cewa matsalar na iya janyo koma baya ga cigaban al’umma da ƙasa gaba ɗaya.
Shugaban NDLEA ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙarfafa matakai domin dakile yaduwar miyagun ƙwayoyi tare da rage buƙatar amfani da su a tsakanin jama’a.
Marwa ya kuma jaddada cewa wajibi ne a ɗauki matakan gaggawa domin dakile wannan matsala, tare da wayar da kan matasa kan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi domin kare makomar ƙasa.