Jam’iyyar APC ta ayyana ranakun 15 da 16 ga watan Mayu, 2026 domin gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, a shirinta na tunkarar zaɓen 2027.
A jadawalin da jam’iyyar ta fitar, za a fara sayar da fom ɗin nuna sha’awa da na takara daga ranar 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, yayin da ranar 4 ga Mayu ita ce wa’adin ƙarshe na miƙa fom ɗin.
Jam’iyyar ta kayyade kuɗin fom ɗin neman takarar shugaban ƙasa zuwa naira miliyan 100, wanda ya haɗa da miliyan 30 na fom ɗin nuna sha’awa da kuma miliyan 70 na fom ɗin takara.
Baya ga na shugaban ƙasa, APC ta tsara gudanar da zaɓen fidda gwani na sauran muƙamai kamar gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki a ranaku daban-daban cikin watan Mayu.
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar na tabbatar da tsari mai kyau da ingantaccen gudanar da zaɓukan cikin gida gabanin babban zaɓen 2027.