Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnatin Katsina ta ƙara wa sarakunan gargajiya albashi

Gwamnatin Katsina ta ƙara wa sarakunan gargajiya albashi Gwamnatin Katsina ta ƙara wa sarakunan gargajiya albashi
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda.

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Umaru Radda ta amince da aiwatar da dokar masarautu da Majalisar Dokokin jihar ta zartar a watan Agustan 2025.

A sakamakon haka, an ɗaga matsayin Hakimai zuwa matakin albashi na 16, yayin da aka ɗaga na Dagatai zuwa mataki na 10.

Gwamna Radda ya bayyana wannan mataki a matsayin wani gagarumin ci gaba da nufin farfaɗo da masarautun gargajiya da kuma inganta jin daɗin shugabannin al’umma, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa ci gaba a matakin ƙasa.

Ya kuma yaba wa Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki bisa tabbatar da nasarar aiwatar da wannan tsari, yana mai cewa ana sa ran ganin amfaninsa a nan gaba kaɗan.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa sarakunan gargajiya, yana mai jaddada cewa haɗin kansu ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use