Jam’iyyar NDC ta ce za ta gudanar da babban taronta na ƙasa a ranar 9 ga watan Mayun 2026, a shirinta na tunkarar zaɓen 2027, yayin da zaɓen fidda gwani zai fara daga 22 ga watan.
A wata wasiƙa da ta aika wa Hukumar Zaben Najeriya ranar 15 ga Afrilu, jam’iyyar ta bayyana sabon jadawalin zaɓenta.
A cewarta, za a yi tarukan mazabu ranar 1 ga Mayu, sannan na kananan hukumomi 2 ga Mayu, jihohi 4 ga Mayu, yankuna 6 ga Mayu, kafin babban taron ƙasa na 9 ga Mayu.
Jam’iyyar ta buƙaci Hukumar Zaben Najeriya ta sanya ido kan dukkan matakai, tana mai cewa za a gudanar da su cikin gaskiya da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.