Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

NDC ta sanar da ranar fara zaɓen fidda gwani

NDC ta sanar da ranar fara zaɓen fidda gwani NDC ta sanar da ranar fara zaɓen fidda gwani
Tambarin jam'iyyar NDC a Najeriya.

Jam’iyyar NDC ta ce za ta gudanar da babban taronta na ƙasa a ranar 9 ga watan Mayun 2026, a shirinta na tunkarar zaɓen 2027, yayin da zaɓen fidda gwani zai fara daga 22 ga watan.

A wata wasiƙa da ta aika wa Hukumar Zaben Najeriya ranar 15 ga Afrilu, jam’iyyar ta bayyana sabon jadawalin zaɓenta.

A cewarta, za a yi tarukan mazabu ranar 1 ga Mayu, sannan na kananan hukumomi 2 ga Mayu, jihohi 4 ga Mayu, yankuna 6 ga Mayu, kafin babban taron ƙasa na 9 ga Mayu.

Jam’iyyar ta buƙaci Hukumar Zaben Najeriya ta sanya ido kan dukkan matakai, tana mai cewa za a gudanar da su cikin gaskiya da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use