Rundunar sojin Najeriya na Operation Enduring Peace sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga biyu a wani samame da suka kai yankin Marit da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:49 na yammacin ranar Talata, 21 ga Afrilu 2026, a kusa da Doruwa Babuje, bayan samun bayanan sirri kan wasu ‘yan bindiga da ke addabar al’ummomi.
Rahotanni sun ce waɗannan ‘yan bindigar na kai hare-hare, yin fyade da kuma satar makamai a yankunan, lamarin da ya jawo damuwa ga mazauna yankin.
Sojojin sun yi wa ‘yan bindigar kwanton ɓauna, inda aka kashe biyu daga cikinsu yayin musayar wuta, wasu kuma suka tsere zuwa cikin dazuka.
An kuma gano makamai d suka hada da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, harsasai biyar da adda da wuka da kuma wayar hannu.
A halin yanzu, dakarun na ci gaba da zama a yankunan Marit da Lajam domin tabbatar da tsaro, yayin da ake farautar sauran ‘yan bindigar da suka tsere.