Tun bayan lokacin da Comrade Aminu Abdussalamu Gwarzo ya yi murabus daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano, ake ta cece-kuce kan wanda zai maye gurbin sa, kuma ya yi tasiri a zaben 2027 da ke tafe.
Daga cikin wadanda ake tunanin za’a nada su wannan kujerar akwai, kakakin majalisar jihar, Isma’il Falgore, Rabi’u Sulaiman Bichi da Murtala Sule Garo.
Duk da cewa jiga-jigan siyasar jihar musamman ‘ya’yan jam’iyyar APC tun asali sun nuna sha’awar su na ganin an nada Garo a wannan kujerar na mataimakin gwamnan jihar Kano.
Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya bayyana cewa, gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya mika sunan tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar a zamanin Ganduje, Murtala Sule Garo don tantancewa a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.