Dakta Emmanuel N. Musa ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a jihar Adamawa, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne bayan abin da ya kira rashin adalci da ya fuskanta a cikin jam’iyyar.
A cikin wata wasiƙar murabus da ya aika wa shugabannin jam’iyyar, Musa ya ce ya yanke shawarar fita daga jam’iyyar ne bayan nazari mai zurfi.
Ya jaddada cewa ya riga ya dakatar da shiga harkokin jam’iyyar tun kafin yanzu, yana mai cewa wannan mataki ya biyo bayan abubuwan da suka faru a cikin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa abubuwan da suka faru a tarukan jam’iyyar na baya-bayan nan, musamman a matakin ƙaramar hukuma da kuma jiha, sun taka muhimmiyar rawa wajen yanke wannan hukunci,.
Ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta.