Gwamnatin ƙasar Norway na shirin gabatar da wani sabon kudirin doka da zai hana yara ‘yan ƙasa da shekaru 16 amfani da kafafen sada zumunta, a wani yunƙuri na kare lafiyar su da tsaron rayuwarsu a yanar gizo.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, gwamnati ta bayyana cewa kudirin dokar zai ɗora alhakin tantance shekarun masu amfani da kafafen sada zumunta a kan manyan kamfanonin fasaha, domin tabbatar da cewa yara ba sa shiga shafukan da ba su dace da shekarunsu ba.
Matakin na Norway ya zo ne a daidai lokacin da ƙasashe da dama a Turai ke ƙoƙarin ƙara tsaurara dokoki kan amfani da kafafen sada zumunta, ciki har da Faransa da Spain.