‘A baya gwamna da duka mukarrabansa na yin biyayya ga Kwankwaso bisa tilas, saboda tare da shi aka kafa gwamnatin, amma yanzu tun da kowa yana bangarensa, dole a bar mu mu yi abin da ya dace ga jama’ar Kano’
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Hussaini ya bayyana haka ne a hirar sa da Explorer Hausa, inda ya bayyana karara yadda madugun kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ke tilasta gwamna da sauran jami’an gwamnati yin abinda yake so.
Hussaini, ya ce, ko a yanzu duk mai tunanin cewa ana bai wa gwamna umarni wajen ayyukan da yake yi, ya sani abu ne mai wahala ka bai wa gwamna irin jihar Kano umarni ya bi, amma ana iya karbar shawarwari.