Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sanata Natasha ta yi alkawarin samar da intanet kyauta wa ‘yan mazabarta

Sanata Natasha ta yi alkawarin samar da intanet kyauta wa 'yan mazabarta Sanata Natasha ta yi alkawarin samar da intanet kyauta wa 'yan mazabarta
Sanata Natasha ta yi alkawarin samar da intanet kyauta wa 'yan mazabarta

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana shirin samar da intanet kyauta a muhimman wurare a mazabarta domin tallafawa matasa.

Ta sanar da haka ne a wani sako da ta wallafa a shafin Facebook bayan ziyarar da ta kai karamar hukumar Idah a Kogi ta Gabas.

A ziyarar, ta hadu da shugabannin jam’iyyar PDP tare da karbar sabbin mambobin da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Ta ce shirin ya samo asali ne daga shawarar wani sabon mamba, Idris HK, wanda ya ba da shawarar samar da intanet kyauta domin taimakawa matasa da ‘yan kasuwa da kuma masu kirkira.

Sanatar ta jaddada cewa za a aiwatar da shirin domin kara samar da ayyukan yi da kuma inganta kirkire-kirkire ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use