Dama dai Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika da sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin jihar domin neman tantancewa a matsayin mataimakinsa.
Hakan na zuwa ne bayan murabus ɗin da Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga watan Maris ɗin 2026.
Wannan dai ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen sheƙa da aka samu tsakanin gwamnan da mataimakinsa da wasu ‘yan majalisar jihar da sauran masu ruwa da tsaki cikin gwamnatin.
Murtala Sule Garo na daga cikin mutane uku da aka yi ta tsammanin gwamnan zai ɗauki mataimakin nasa a cikinsu.
Wasu ɓangarorin jam’iyyar APC, musamman magoya bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, sun nuna adawa da hakan, sakamakon tsohuwar takaddama ta siyasa tsakanin su.
An rawaito cewa Barau na goyon bayan wani ɗan takara na daban.
A baya dai, hukumar EFCC ta taba binciken Sule Garo kan zargin almundahana a lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi da masarautu a ƙarƙashin gwamnatin Ganduje.