Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya

Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya
Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya mayar da martani kan damuwar da ake yi game da rahotannin rufe Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, inda ya danganta matakin da fargabar tsaro ta duniya, ba matsalar siyasar cikin gida ba.

A cikin sabuwar sanarwar gargadin tafiye-tafiye, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa matakin ya fara aiki ne daga ranar 8 ga Afrilu, 2026.

Ta kuma shawarci ‘yan ƙasar Amurka da su sake tunani kafin su yi tafiya zuwa Najeriya, sakamakon karuwar matsaloli da suka haɗa da aikata laifuka, ta’addanci, sace-sace, rikice-rikicen cikin gida da kuma rashin daidaiton ingancin harkokin lafiya.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da sabon hedikwatar NRS a Abuja, Akpabio ya yi watsi da zargin cewa ana rufe ofisoshin jakadanci ne saboda zaɓen Najeriya, yana mai cewa irin wannan fahimta ba ta da tushe.

Ya bayyana cewa ƙasashe kamar Amurka na iya ɗaukar irin waɗannan matakan kariya a matakin duniya, musamman saboda ƙaruwar zaman ɗar-ɗar da ke tsakaninsu da wasu ƙasashe kamar Iran.

Haka kuma, ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji danganta irin waɗannan matakai da siyasar cikin gida, musamman batun zaɓe.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use