Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Jam’iyyar ADC ta kori Nafi’u Bala da Leke Abejide

Jam’iyyar ADC ta kori Nafi’u Bala da Leke Abejid Jam’iyyar ADC ta kori Nafi’u Bala da Leke Abejid
Jam’iyyar ADC ta kori Nafi’u Bala da Leke Abejid

Jam’iyyar ADC ɓangare David Mark ta sanar da korar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ta shi’ar Arewa maso gabas Nafi’u Bala da ɗan majalisa Leke Abejide.

waɗanda aka kora sun haɗa da shugaban jam’iyyar a jihar Abia, Kenneth Ehiator, da kuma Dumebi Kachikwu, Stella Chukwu da Elias Adiukwu.

A yayin taron, ɓangaren shugabancin da ke biyayya ga tsarin David Mark ya kuma tabbatar da naɗin Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar, tare da Babachir Lawal da Bolaji Abdullahi da sauran mambobin kwamitin gudanarwa.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Nafi’u Bala ya ayyana kansa a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar.

Sai dai kuma, Kotun Koli ta sanya ranar 22 ga watan Afrilu domin sauraron ƙarar rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use