Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Onanuga ya zargi Sakataren ADC Aregbesola da rashin kawo ci ga ba a Osun

Onanuga ya zargi Sakataren ADC Aregbesola da rashin kawo ci ga ba a Osun Onanuga ya zargi Sakataren ADC Aregbesola da rashin kawo ci ga ba a Osun
Onanuga ya zargi Sakataren ADC Aregbesola da rashin kawo ci ga ba a Osun

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya soki sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, kan sukar da ya yi wa gwamnatin Tinubu.

A yayin taron jam’iyyar ADC ta kasa a Abuja, Aregbesola ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza cika alkawuran da ta dauka karkashin shirin “Renewed Hope”, yana mai cewa babu wani gagarumin sauyi da aka samu cikin shekaru uku.

Sai dai Onanuga ya musanta hakan, yana mai cewa kalaman Aregbesola ba gaskiya ba ne tare da zarginsa da barin tulin bashi a lokacin da yake gwamna a jihar Osun.

Ya kuma jaddada cewa a lokacin da Aregbesola ke ministan harkokin cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari, an fuskanci matsalolin tsaro da suka hada da fasa gidajen yari.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use