Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da wani bidiyo inda ta ba da wa’adin awanni 72 kan makomar mutane 416 da ta sace a Jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda aka sace sun haɗa da mata da yara daga yankin Ngoshe, a ƙaramar hukumar Gwoza, waɗanda ke hannun ‘yan ta’addan tun bayan wani hari da suka kai a yankin.
A cikin bidiyon, ƙungiyar ta yi barazanar kashe mutanen idan ba a biya buƙatunta ba, tare da gargadin cewa duk wani yunƙurin ceto su da ƙarfin tuwo na iya jefa rayukansu cikin haɗari.
Haka kuma, an ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun nemi kuɗin fansa mai yawa kafin sakin waɗanda aka sace, abin da ya ƙara tsananta fargaba da tashin hankali a yankin.
A halin yanzu, ana ci gaba da kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta ɗaukar matakan gaggawa domin ceto rayukan waɗanda ke hannun ‘yan ta’addan.