Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

UAE ta ce ta bankado wata ƙungiyar ta’addanci mai Alaƙa da Iran

UAE ta ce ta bankado wata ƙungiyar ta’addanci mai Alaƙa da Iran UAE ta ce ta bankado wata ƙungiyar ta’addanci mai Alaƙa da Iran
UAE ta ce ta bankado wata ƙungiyar ta’addanci mai Alaƙa da Iran

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE ta sanar da cewa ta rusa wata ƙungiyar da ake zargi da ta’addanci mai alaƙa da Iran, wadda ake zargin tana shirin aiwatar da ayyukan ɓarna a cikin ƙasar.

Hukumar Tsaron Ƙasa ta UAE ta bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta cewa ta kama wasu mambobin wannan ƙungiya, waɗanda ake zargi da ƙoƙarin “lalata haɗin kai da zaman lafiya” a ƙasar.

Hukumar ta ƙara da cewa wannan ƙungiyar da ake kira ta’addanci na ƙoƙarin jawo hankalin matasa domin shiga cikinta, tare da shirya ayyukan ɓarna cikin tsari a cikin iyakokin ƙasar.

Bugu da ƙari, an ce ƙungiyar na tattara kuɗaɗe daga cikin ƙasar sannan tana tura su zuwa ƙasashen waje.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use