Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

EU na shirin faɗaɗa takunkumi kan Iran saboda rikicin mashigar Hormuz

EU na shirin faɗaɗa takunkumi kan Iran saboda rikicin mashigar Hormuz EU na shirin faɗaɗa takunkumi kan Iran saboda rikicin mashigar Hormuz
EU na shirin faɗaɗa takunkumi kan Iran saboda rikicin mashigar Hormuz

Ƙungiyar Tarayyar Turai na shirin faɗaɗa takunkuminta kan Iran domin haɗa duk waɗanda ake zargi da hana zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Jami’an diflomasiyya sun bayyana cewa an cimma matsaya don hukunta mutane da kamfanonin da ke da hannu wajen toshe wannan muhimmiyar hanya ta ruwa.

Wannan mataki na zuwa ne bayan Iran ta rufe mashigar sakamakon rikicin yaƙi, lamarin da ya shafi kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya.

Ana sa ran ƙarin sunayen waɗanda za a kakabawa takunkumi cikin makonni masu zuwa, yayin da rikicin ke ci gaba da tayar da hankalin duniya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use