Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

CBN ya ƙara kuɗin katin ATM zuwa N1,500

CBN ta ƙara kuɗin katin ATM zuwa N1,500 CBN ta ƙara kuɗin katin ATM zuwa N1,500
CBN ta ƙara kuɗin katin ATM zuwa N1,500

Babban Bankin Najeriya, (CBN), ya sanar da ƙarin kuɗin yin ko sauya katin ATM zuwa naira 1,500 daga naira 1,000, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 50 cikin 100.

Hakan na kunshe ne a cikin sabon daftarin dokokin cajin bankuna na shekarar 2026, wanda aka fitar domin daidaita tsarin kuɗaɗen da cibiyoyin kuɗi ke karɓa a ƙasar.

Sai dai a wani mataki na sauƙaƙa wa kwastomomi, CBN ta soke cajin kulawa na wata-wata na katin ATM naira 50 da ake cirewa daga asusun masu amfani da katin naira.

Duk da haka, bankin ya bayyana cewa masu amfani da katunan kuɗin waje za su ci gaba da biyan kuɗin kulawa na dala 10 a shekara.

Haka kuma, sabon tsarin ya tanadi cewa kuɗin amfani da POS wajen biyan kaya ko sabis zai kasance nauyin ‘yan kasuwa ne, ba na masu amfani da kati ba, domin ƙarfafa tsarin biyan kuɗi na zamani.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use