An samu rudani a Najeriya bayan wani tsarin fasahar zamani (AI) ya nuna cewa wani asusun X mai rikitarwa na da alaƙa da shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), lamarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a.
Rahotanni sun bayyana cewa AI da Grok ya tabbatar da cewa asusun X ɗin da aka kirkira tun 2022 yana da alaƙa da sunan shugaban INEC, kafin daga bisani a sauya sunansa bayan rikicin ya ɓarke.
Sai dai a wani ɓangare, shugaban INEC ya musanta mallakar kowane asusun X, yana mai cewa wannan zargi ƙirƙira ne, tare da zargin cewa wasu masu aikata laifukan yanar gizo ne ke amfani da sunansa domin yaudarar jama’a.
Lamarin ya ƙara ɗaukar zafi ne bayan wasu tsofaffin saƙonni da ke nuna goyon bayan siyasa sun bayyana daga asusun, abin da ya sa wasu ‘yan ƙasa da ƙungiyoyi ke kira da a binciki lamarin tare da ɗaukar mataki.
Masana da masu sa ido kan harkokin dimokuraɗiyya na ganin cewa wannan rikici na iya shafar amincewar jama’a ga sahihancin hukumar zaɓe, musamman idan ba a warware batun cikin gaskiya da gaskiya ba.