Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gobara ta ƙone buhunan albasa na naira miliyan 56.8 a Sokoto

Albasa

Manoman albasa a jihar Sokoto sun shiga cikin damuwa bayan wata gobara ta lalata buhunan albasa sama da 2,275 a kauyen Kojiyo da ke Karamar Hukumar Goronyo, inda aka kiyasta asarar kudinsu ta kai naira miliyan 56.8.

Gobarar ta kona rumbunan adana albasa na gargajiya kusan 65, lamarin da ya lalata babbar hanyar samun kuɗin al’ummar yankin da suka dogara da noma.

Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2 na rana a ranar Juma’a, kuma ta shafe kusan sa’o’i bakwai tana ci kafin a shawo kanta. Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, amma al’ummar yankin sun yi asarar dukiya mai yawa.

Shugaban kungiyar masu noma, sarrafawa da kasuwancin albasa ta Najeriya, Aliyu Isah Maitasamu, ya ce kowanne rumbu na dauke da matsakaicin buhuna 35 na albasa.

Ya ce jimillar buhunan da suka kone sun kai 2,275, inda kowanne buhu ke da darajar kimanin naira 25,000 a kasuwa, wanda ya kai jimillar asarar zuwa naira miliyan 56.8.

Ya kuma kara da cewa har yanzu ana bincike domin gano musabbabin gobarar, yana mai jaddada kira ga gwamnati da hukumomin agaji su tallafa wa manoman da abin ya shafa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use