Kotun Jihar Kaduna ta ɗage ci gaba da sauraron buƙatar neman beli na tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, inda ta tsara cewa za a ci gaba da shari’ar a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2026.
Alkalin kotun ya bayyana cewa an ɗage zaman ne domin bai wa ɓangarorin da ke shari’ar damar kammala gabatar da hujjoji da shaidu yadda ya kamata, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin shari’a cikin tsari.
A baya, Hukumar EFCC ta kama El-Rufa’i bisa wasu zarge-zarge da ake masa, kafin daga bisani ta sake shi, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin.
Sai dai jim kaɗan bayan hakan, Hukumar ICPC ta sake cafke shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda goma da suka haɗa da zargin almundahana da kuma karkatar da kadarorin gwamnati.
A halin yanzu, ICPC na ci gaba da tsare shi yayin da ake jiran ranar da kotu za ta ci gaba da sauraron buƙatar belinsa, lamarin da ke jawo hankalin jama’a da masu bibiyar harkokin siyasa a ƙasar.