Tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya zargi shugaban ƙasa Bola Tinubu da yin amfani da iko wajen takura wa jam’iyyun hamayya a ƙasar Nigeria.
Peter Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta ARISE a ranar litini, inda ya ce hana jam’iyyarsa ta ADC gudanar da babban taronta a Abuja na nuna ƙoƙarin tauye ‘yancin siyasa da kuma rage ƙarfin dimokuraɗiyya a ƙasar.
Ya ƙara da cewa jam’iyyun hamayya suna da cikakken haƙƙi bisa kundin tsarin mulki na ƙasa na gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci, amma ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na nuna rashin goyon baya ga hakan.
A cewarsa, irin waɗannan matakai na iya haifar da rauni ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya, musamman idan aka ci gaba da takura wa ‘yan adawa wajen gudanar da harkokinsu na siyasa.
Duk da haka, Peter Obi ya jaddada cewa duk wani ƙoƙari na hana su gudanar da tarukan jam’iyya ba zai dakatar da su daga ci gaba da shirye-shiryensu ba, yana mai cewa za su gudanar da babban taronsu kamar yadda aka tsara.