Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Manoma za su amfana kai tsaye da bashin $500m — Atama

Manoma za su amfana kai tsaye da bashin Manoma za su amfana kai tsaye da bashin
Emmanuel Atama, Babban sakataren hukumar bayar da lamuni ga kungiyoyin haɗin gwiwa ta Najeriya (NCFAN).

Babban sakataren hukumar bayar da lamuni ga Ƙungiyoyin haɗin gwiwa ta Najeriya (NCFAN), Emmanuel Atama, ya tabbatar da cewa bashin dala miliyan 500 da aka tanada domin tallafa wa manoma miliyan ɗaya, zai isa hannun manoma na gaskiya, ba tare da tsoma bakin ‘yan siyasa ba.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust TV, Atama ya bayyana cewa dalilin da ya sa shirye-shiryen tallafin baya suka gaza cimma buri shi ne rashin isasshen tsari da kuma katsalandan ɗin ‘yan siyasa.

Ya kuma ce, tun bayan ƙaddamar da wannan sabon shiri, an fara wayar da kan manoma a dukkan matakan ƙananan hukumomi, tare da ƙarfafa su su shiga ta hanyar ƙungiyoyin haɗin gwiwa domin samun sauƙin cin gajiyar shirin.

Bugu da ƙari, Atama ya jaddada cewa za a bayar da bashin ne a cikin kayan noma maimakon kuɗi kai tsaye, domin tabbatar da an yi amfani da tallafin yadda ya dace da kuma kauce wa duk wani amfani da ba shi da alaƙa da noma.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use