Donald Trump ya nuna yiwuwar sake fara sabbin tattaunawar Amurka da Iran a ƙasar Pakistan, yayin da ake ci gaba da kokarin sulhu tsakanin bangarorin biyu.
A cewarsa, ana iya ci gaba da tattaunawar cikin kwanaki biyu masu zuwa, inda ya nuna cewa Pakistan na iya sake karɓar bakuncin tattaunawar.
Trump ya bayyana cewa akwai yiwuwar hakan ne saboda rawar da Pakistan ke takawa wajen shiga tsakani a rikicin.
Ya kuma yaba wa shugaban sojojin Pakistan, Asim Munir, yana mai cewa yana yin aiki mai kyau a kokarin tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar New York Post daga Islamabad.