Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Rashin tsaro zai kare bayan zabe — Godswill Akpabio

Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya
Akpabio ya danganta rufe ofishin jakadancin Amurka da matsalolin tsaro na duniya

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya danganta karuwar rashin tsaro a kasar da shirye-shiryen zabukan da ke tafe, yana mai cewa za a samu sauyi bayan zabe.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da hedikwatar Hukumar Haraji ta Najeriya a Abuja a ranar Talata, Akpabio ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yin aiki mai kyau, kuma masu adawa da gwamnati na amfani da rashin tsaro domin tayar da hankali.

Ya kara da cewa da zarar an kammala zabe, matsalar rashin tsaro za ta zama tarihi cikin kankanin lokaci.

Haka kuma, ya soki ‘yan adawa, yana mai cewa suna cikin rudani, inda ya yi nuni kai tsaye ga Peter Obi, yana cewa wasu da suka samu kuri’u miliyan shida sun bar jam’iyyarsu suna neman wata dandalin siyasa.

A karshe, ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin da ke mulki, yana mai cewa tana kan hanya madaidaiciya wajen gudanar da ayyukanta.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use