Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi kakkausar gargadi ga al’ummar jihar da su guji bai wa ’yan ta’adda duk wani nau’i na taimako, yana mai jaddada cewa duk wanda aka kama da hannu a irin wannan aiki za a ɗauke shi a matsayin abokin gaba.
Zulum ya bayyana cewa akwai wasu daga cikin mazauna da ke bai wa masu tayar da ƙayar baya mafaka, bayanan sirri, ko kuma tallafin kayan aiki, abin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a yankin.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na aiki tuƙuru tare da jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar, tare da roƙon jama’a da su riƙa bayar da sahihan bayanai ga hukumomi domin taimaka wa ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ’yan ta’adda.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta.
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da yankin Arewa maso Gabas ke ci gaba da fuskantar hare-hare, inda ƙungiyar Boko Haram ke cigaba da addabar al’umma da tashe-tashen hankula.