Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da na tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, sun kaddamar da sabuwar tafiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK) Movement domin ƙarfafa haɗin kan ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027.
An bayyana ƙaddamar da tafiyar ne a Abuja, inda aka ce an riga an fara shimfiɗa tsare-tsare a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, tare da naɗa wakilai a matakan jiha da shiyya don gudanar da ayyukan wayar da kai.
Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Justin Ijeh, ya ce haɗakar ta haɗa mambobi daga Obidient Movement, Kwankwasiyya Movement, NNPP da kuma African Democratic Congress (ADC), domin ƙarfafa hadin gwiwar siyasa.
Ya bayyana cewa matsalolin tattalin arziki, tsadar rayuwa da rashin tsaro ne suka sa aka kafa wannan dandali, wanda ke da nufin samar da sabon salo a siyasar Najeriya.
A cewarsa, OK Movement na da burin zama wata kafa ta haɗin kai da za ta ba da gudunmawa wajen gina sabuwar makomar siyasa a ƙasar gabanin babban zaɓen 2027.