Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Harin Boko Haram ya kashe kwamandan soji da wasu jami’ai a Borno

Harin Boko Haram ya kashe kwamandan soji da wasu jami’ai a Borno Harin Boko Haram ya kashe kwamandan soji da wasu jami’ai a Borno
Harin Boko Haram ya kashe kwamandan soji da wasu jami’ai a Borno

Wani mummunan hari da mayaƙan Boko Haram suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya tare da wasu jami’ai shida a Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa Kanal I.A. Mohammed, kwamandan bataliya ta 242 da ke Munguno, ya rasa ransa ne sakamakon wani bam da ya tashi a lokacin da su ke gaggawar kai dauki bayan samun kiran cewa an kai hari kan wasu sojoji a bakin aiki.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin rundunar sojin saman Najeriya da jefa bama-bamai a kasuwar Jilli, lamarin da aka ce ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 200, ciki har da ‘yan kasuwa.

Harin na Munguno ya biyo bayan wani makamancin hari da aka kai kwanaki uku da suka gabata a yankin Benisheikh, inda aka kashe wani babban jami’in soja, Birgediya Oseini Braimah, tare da wasu jami’ai 17, abin da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use