Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Babu wanda zai hana taron ADC – Dino Melaye

Babu wanda zai hana taron ADC – Dino Melaye Babu wanda zai hana taron ADC – Dino Melaye
Babu wanda zai hana taron ADC – Dino Melaye

Mamba a kwamitin shirya babban taron jam’iyyar ADC, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa babu wani ƙarfi da zai iya hana jam’iyyar gudanar da taronta kamar yadda aka tsara.

Ya ce duk da wasu ƙoƙarin da ake yi na hana su amfani da wurin taron, jam’iyyar ta kammala dukkan sharuddan da suka dace, ciki har da samun sahihin yarjejeniya da kuma biyan kuɗaɗen da ake buƙata.

Melaye ya jaddada cewa ADC ba za ta ja da baya ba, yana mai cewa an shirya tsaf domin gudanar da taron cikin tsari da lumana, duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Haka kuma, ya bayyana cewa jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a faɗin ƙasar, tare da nuna aniyarta ta kalubalantar jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use