Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Fasahar AI za ta taimaka wajen magance ƙalubalen Najeriya - Pantami
Kalaman Atiku kan harin Jilli za su iya siyasantar da lamarin tsaro – Fadar Shugaban Najeriya
Babu wanda zai hana taron ADC – Dino Melaye

Kalaman Atiku kan harin Jilli za su iya siyasantar da lamarin tsaro – Fadar Shugaban Najeriya

Dole Tinubu ya yi wa'adi biyu a mulki – Fadar shugaban kasa Dole Tinubu ya yi wa'adi biyu a mulki – Fadar shugaban kasa
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Fadar Shugaban Najeriya ta yi kakkausar suka ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, bayan ya soki harin jirgin sojin a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin asarar rayuka kusan 200 in ji mazauna yankin tare da raunata da dama.

Fadar ta bayyana cewa kalaman Atiku na iya jawo rudani da siyasantar da batun tsaro, tana mai cewa ya kamata a bar hukumomin da abin ya shafa su kammala bincike kafin yanke hukunci kan lamarin.

A cewar rahotanni, harin ya faru ne bayan wasu jiragen soji sun kai farmaki kan kasuwar Jilli a ranar Asabar ko da ya ke rundunar sojin najeriya ta ce ta kai hari a Jilli amma kan ‘yan ta’adda ne da kuma maboyarsu.

Jim kadan bayan fitar labarin ne Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da lamarin tare da kira ga gwamnati ta tabbatar da gaskiya da adalci, tare da ɗaukar matakan da za su hana sake aukuwar irin wannan kuskure a nan gaba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use